<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>458</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ku zo mutane duk
 Ku furta laifofinku yau
 A gaban Yesu Mai Ceto,
 Shi zai yi gafara .

[V2]
 2) Idan da zafin kishi yau
 Cikin masu bin Yesu.
 Ba za su yi albarka ba
 Idan da kishin nan.

[V3]
 3) Ƴanuwa, ku bar kishi
 Ku bar ƙeta, ku bar ƙarya
 Ku bar zina, ku bar gulma
 Ku bi Mai Cetonmu.

[V4]
 4) Idan da waɗannan abu
 A cikin zukatanmu yau
 Me za mu ce ma Yesu
 Ran da mun kai sama?

[V5]
 5) Shi zai ce ku tashi nan
 Ku tashi nan, ku tashi nan
 Shi zai ce ku tashi nan
 Ni dai ban san ku ba.

[V6]
 6) A ranan nan sai kumya
 Kumya mar-iyaka
 Sai kuka mai zafi kuwa
 Da cizon haƙora.

[V7]
 7) Masu bi, mu yi anniya
 Domin ranar zuwansa
 Zai ce da mu bayin kirki
 Ku shiga murnarku.

[V8]
 8) Taimake mu, ya Yesu
 Ka bi da mu da Ruhunka
 Domin mu aika nufinka
 Har ran da za ka zo.

[V9]
 9) Halleluya ga Yesu
 Ga Yesu Mai Cetonmu.
 Halleluya ga Yesu, halleluya Amin
 Ga Yesu Mai Ceto.</lyrics>
<title>Ku Zo Mutane Duk LW458</title>
</song>